Rundunar ƴan sandan Najeriya ta gargadi masu shirin gudanar da zanga-zanga domin neman a saki Mazi Nnamdi Kanu da kada su kusanci Aso Rock da muhallin da ke kewaye da shi. Kakakin rundunar, CSP Benjamin Hundeyin, ya bayyana cewa gargadin ya biyo bayan umarnin kotun tarayya da ta hana duk wani irin gangami a kusa da fadar shugaban ƙasa da wasu muhimman wurare a Abuja.
Kotun ta bayar da wannan umarni ne a ranar 17 ga Oktoba a shari’ar da ake yi tsakanin Gwamnatin Tarayya da Omoyele Sowore da wasu mutum huɗu. Wuraren da aka haramta zanga-zanga sun haɗa da Aso Rock, Majalisar Tarayya, Hedikwatar ƴan sanda, Kotun Daukaka Kara, Eagle Square da Shehu Shagari Way. Rundunar ƴan sandan ta shawarci masu zanga-zanga da kada su kusanci waɗannan wurare kuma su guji duk wani abin da zai haifar da tashin hankali.
Hundeyin ya ce rundunar ta tanadi tsauraran matakan tsaro domin kare rayuka da dukiyoyi da kuma tabbatar da zaman lafiya. Ya gargadi duk wanda zai yi amfani da zanga-zanga a matsayin ɓoye-ɓoye don haddasa rikici, ɗaukar makamai ko lalata kadarori cewa za a kama su, a gudanar da cikakken bincike kuma a gurfanar da su bisa doka, har da dokokin ta’addanci idan ya dace.
Ya ƙara da cewa rundunar za ta bi duk masu tada hankali a kafafen sada zumunta ta hanyar amfani da shaidar dijital domin gurfanar da su. Sufeto Janar na ƴan sanda, Kayode Egbetokun, ya umarci kwamishinan ƴan sanda na Babban Birnin Tarayya da hukumomin tsaro su tabbatar da bin umarnin kotu, tare da tabbatar da tsaron al’umma da ci gaban ayyuka a Abuja.

