Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa bai taɓa ƙoƙarin sauya addinin matarsa, Sanata Oluremi Tinubu, daga Kiristanci zuwa Musulunci ba.
Tinubu ya bayyana haka ne a wurin bikin jana’izar Nana Lydia Yilwatda — mahaifiyar shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda — da aka gudanar a Jos, babban birnin Jihar Filato, ranar Asabar.
Ya yi kira ga al’ummar Filato da ’yan Najeriya gaba ɗaya da su zauna lafiya tare da guje wa banbancin addini da kabilanci.
“Ni musulmi ne, gadarsa na yi, amma matata Fasto ce, kuma tana yi min addu’a a ko da yaushe. Ban taɓa neman ta sauya addininta ba. Ina mutunta ’yancin kowa na bin addinin da ya zaɓa,” in ji Tinubu.
Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya gode wa shugaban ƙasa saboda halartar jana’izar duk da cunkoson aikinsa, tare da bayyana cewa gwamnati na ƙoƙari wajen tabbatar da zaman lafiya a jihar.
A nasa jawabin, Farfesa Nentawe ya bayyana mahaifiyarsa a matsayin mace mai jajircewa, tausayi da sadaukarwa, wadda ta rayu wajen taimakon al’umma.

