Wani rahoto daga Saturday PUNCH ya bayyana cewa wasu jami’an Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) sun fara neman manyan ‘yan Najeriya domin a ɗauke su a matsayin jami’an tsaro na musamman (VIP escorts), bayan umarnin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na janye ‘yan sanda daga rakiyar manyan mutane da ‘yan siyasa. Umarnin, wanda aka bayar a ranar 24 ga Nuwamba, an ce an yi shi ne domin mayar da hankali kan yaƙi da garkuwa da mutane da sauran matsalolin tsaro a sassan ƙasar nan, musamman Arewa.
Rahoton ya ce bayan janyewar ‘yan sanda sama da 11,566 daga ayyukan VIP, manyan mutane sun fara neman taimakon NSCDC da kamfanonin tsaro masu zaman kansu. A gefe guda kuma, wasu jami’an DSS—musamman na ƙananan matsayi—sun fara kusantar wasu VIP domin su nemi a tura su a matsayin sababbin masu tsaro. Sai dai wasu manyan jami’an DSS sun bayyana cewa akwai tsauraran ƙa’idoji kan irin wannan tura aiki, inda aka ce ba a yarda a tura jami’ai sama da matakin Level 13 ga VIP sai dai ga gwamnoni ko Fadar Shugaban Ƙasa.
Wannan mataki ya haifar da karuwar buƙata ga kamfanonin tsaro masu zaman kansu, inda masu ruwa da tsaki suka ce neman masu rakiya ya tashi daga kusan kashi 20% zuwa sama da 70% a wasu wurare. Duk da cewa yawancin jami’an tsaron masu zaman kansu ba sa ɗauke da makamai, VIP da dama sun fi son tafiya tare da masu kwarewar tsaro maimakon tafiya su kaɗai, musamman wajen zirga-zirgar tsakanin jihohi.
A gefe guda, Majalisar Dattawa ta bayyana cewa ba ta da shirin neman kariyar tsaro ta musamman ga ‘yan majalisa baki ɗaya, inda ta bukaci kowa ya bi tsarin da Shugaban Ƙasa ya tanada ta hanyar tuntuɓar NSCDC. Haka kuma, wasu kungiyoyin tsaro sun yi gargadin cewa duk wani hari ko garkuwa da wani babban jami’i na iya tayar da hankalin jama’a, tare da kira ga gwamnati da ta magance matsalar tsaro tun daga tushe.

