Hukumar tsaro ta farin kaya, wato DSS, ta kama wani matashi mai suna Innocent Chukwuma, wanda ya yi kira ga rundunar sojin Najeriya da su kifar da gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu. Chukwuma, wanda ke amfani da sunan @TheAgroman a dandalin X (tsohon Twitter), ya wallafa sakonni masu zafi inda ya nemi sojoji su “soke gwamnatin Najeriya” tare da “kafa sabuwar gwamnati”.
Rahotanni sun nuna cewa jami’an DSS sun bi sawunsa har zuwa Oyigbo, a Jihar Rivers, inda suka cafke shi. A cikin sakonninsa, Chukwuma ya zargi gwamnatin da cewa “ta sayar da ƙasar ga kasashen yamma”, yana mai cewa “sojoji ne kaɗai za su iya sake daidaita Najeriya.” Wannan furuci nasa ya janyo cece-kuce a kafafen sada zumunta, inda mutane da dama suka yi Allah-wadai da kiran juyin mulkin.
A ‘yan kwanakin nan, ana ta rade-radin zargin shirin juyin mulki a kasar, har ma aka ce an soke bikin cikar Najeriya shekara 65 da samun ‘yancin kai saboda tsoron hakan. Sai dai Hedikwatar Tsaron Najeriya (DHQ) ta fito ta karyata wannan jita-jita, tana mai cewa babu wani yunƙurin kifar da gwamnati a halin yanzu.
Tun bayan da Shugaba Tinubu ya sauke hafsoshin tsaro a makon da ya gabata, batun juyin mulki ya sake daukar zafi a kafafen sada zumunta. DSS ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da sa ido kan duk wanda ke yada bayanan da ka iya tayar da hankali ko kawo cikas ga tsarin dimokuraɗiyya a Najeriya.

