Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana shirin kafa wata sabuwar rundunar sa-kai makamanciyar Hisbah karkashin Ganduje Foundation, domin ɗaukar tsofaffin jami’ai 12,000 da gwamnatin jihar ta sallama. Ganduje, wanda ya kasance tsohon shugaban APC na ƙasa, ya ce korar jami’an ta kasance rashin adalci, inda aka gabatar masa da rahoton tantance su daga kwamitin Dr. Baffa Babba Dan-Agundi.
Rahoton ya tabbatar da sunaye da bayanan tuntuɓar waɗanda aka kora, tare da bayyana cewa za su kasance tare da Ganduje a sabon tsarin. Ganduje ya ce rundunar za ta yi aiki ne ba a matsayin hukuma ta gwamnati ba, sannan za ta kasance mai zaman kanta da sunan Independent Hisbah, tare da yiwuwar ɗaukar ƙarin masu son shiga daga cikin al’umma.
Manyan jiga-jigan APC sun halarci taron, ciki har da Dr. Nasiru Yusuf Gawuna, Murtala Sule Garo, Abdullahi Abbas da Rabiu Sulaiman Bichi. An kuma bayyana cewa tsohon kwamandan Hisbah, Sheikh Muhammad Harun Ibn Sina, shi ne ake sa ran zai jagoranci sabuwar rundunar, wadda aka ce za ta yi ayyukan wa’azi, taimako, bayar da agajin gaggawa da “hankyatar da alheri da hani ga mummuna.”
Ibn Sina ya ce rundunar — wadda za ta kasance da suna Khairun Nas — ba zata yi takarar hukuma ba, kuma ba lallai ta biya albashi ba, sai dai tana iya samun tallafi daga mutane ko ƙungiyoyi domin biyan ɗan kuɗin alawus. Ya kara da cewa shirin bai kammala kafuwa ba tukuna, amma zai kasance a buɗe ga kowa da kowa ba wai ga waɗanda aka sallama kaɗai ba.

