Gwamnan Jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya tsige dukkan kwamishinoni da sauran manyan jami’an gwamnati da ke cikin gwamnatinsa, bisa ga hukuncin Kotun Koli.
Kakakin gwamnan, Nelson Chukwudi, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Fatakwal a daren Laraba, inda ya ce matakin ya fara aiki nan take.
A wani taron bankwana da aka gudanar tare da majalisar zartarwa a matsayin wani zama na bikin cikar Najeriya shekaru 65 da samun ’yancin kai, Gwamna Fubara ya gode wa tsoffin kwamishinonin bisa gudummawar da suka bayar ga ci gaban jihar cikin shekaru biyu da suka gabata.
Ya kuma yi kira ga ’yan Najeriya da su haɗa kai da Shugaban Ƙasa wajen gina Najeriya tare da tabbatar da zaman lafiya, tsaro da ci gaba, da kuma tabbatar da makoma mai kyau ga al’umma. Gwamnan ya jaddada cewa zai ci gaba da gudanar da mulki da ƙwarin gwiwa, tare da godewa mutanen Rivers bisa goyon bayan da suke ba shi.
A baya-bayan nan, tsohon mai rikon gwamnatin jihar, Vice Admiral Ibok-Ete Ibas (ritaya), ya dakatar da kwamishinonin Fubara da sauran jami’an gwamnati a lokacin da aka kafa dokar ta-baci a jihar. Tun bayan saukarsa daga mulki a ranar 18 ga Satumba, makomar wadannan mukarraban Fubara ta kasance cikin rudani, lamarin da ya sa majalisar dokokin jihar ta bukaci gwamnan ya gabatar da sabbin sunayen kwamishinoni domin tantancewa tare da kasafin kuɗin shekarar 2025.

