Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sanya hannu kan dokar kasafin kuɗin shekarar 2026 da aka gyara, mai jumillar Naira tiriliyan 1.477, inda ya sha alwashin aiwatar da shi gaba ɗaya domin inganta rayuwar al’ummar jihar. Gwamnan ya yi wannan jawabi ne a ranar Laraba, 31 ga Disamba, 2025, jim kaɗan bayan amincewa da kasafin.
Ya bayyana cewa kasafin 2025 ya samu aiwatarwa sama da kashi 80 cikin 100, musamman a bangaren ayyukan raya kasa, ilimi da lafiya. A cewarsa, kasafin 2026 ya fi mayar da hankali kan gina manyan ababen more rayuwa da inganta ayyukan gwamnati, tare da kira ga mambobin majalisar zartarwa da su ƙara jajircewa wajen cimma manufofin gwamnatinsa.
Gwamna Yusuf ya ce Majalisar Dokokin Jihar Kano ta ƙara adadin kasafin daga Naira tiriliyan 1.3 zuwa Naira tiriliyan 1.477 bayan cikakken bincike, inda kashi 71 cikin 100 aka ware wa ayyukan ci gaba, yayin da kashi 29 cikin 100 ya tafi kan kashe-kashen yau da kullum. Ya kuma tabbatar da cewa za a yi amfani da kuɗaɗen kasafin yadda ya dace, domin amfanin al’ummar Kano baki ɗaya.

