Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar PDP a daren Litinin, 4 ga Nuwamba 2025. Ya bayyana hakan ne ta shafinsa na X, inda ya wallafa kwafin takardar murabus dinsa da ya aikewa jam’iyyar, lamarin da ya girgiza siyasar Osun.
Adeleke ya danganta ficewarsa da rikicin cikin gida da ya addabi jam’iyyar, yana mai cewa matsalolin sun yi tsanani har ya ga dacewar ya kauce. A cewarsa, wannan mataki ne da ya yanke bisa la’akari da halin da PDP ke ciki a yanzu.
Gwamnan ya gode wa jam’iyyar bisa damar da ta ba shi a siyasar kasar, tun daga kasancewarsa Sanata mai wakiltar Osun West daga 2017 zuwa 2019, har zuwa zama Gwamnan jihar Osun. Ya ce wannan tarihin ba zai goge daga zuciyarsa ba.
Duk da wannan babban mataki, Adeleke bai bayyana jam’iyyar da zai koma ba. Al’ummar Osun da masana siyasa kuwa na ci gaba da sa ido kan matakin da zai dauka bayan barin PDP.

