Gwamnatin Nasarawa ta bayyana cewa tana shirin kafa rundunar ’yan sandan jiha idan aka kammala sauye-sauyen kundin tsarin mulki da ake tattaunawa a yanzu. Wannan bayani ya fito ne daga kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, CP Usman Baba, yayin taron manema labarai da aka gudanar a Lafia, ranar Litinin.
Ya ce tun daga shekarar 2019, gwamnatin Abdullahi Sule ta mayar da hankali kan tsaro ta hanyar samar da motocin aiki, kayan aiki da sauran kayayyakin tallafi ga jami’an tsaro. Sai ya kara da cewa manufar gwamnan ita ce tabbatar da cewa Nasarawa ta kasance wuri mai kwanciyar hankali da jan hankalin masu zuba jari.
Bechi Huasa ta tattaro cewa gwamnatin ta kuma tura jami’an tsaro zuwa makarantu da wuraren ibada a manyan birane da kananan hukumomi 13 na jihar domin kare rayuka da dukiyoyi. Haka kuma ana aiki da jami’an tsaro, ’yan sa kai da masu sa ido a unguwanni wajen dakile matsalar garkuwa da mutane.
Kwamishinan ya gargadi masu aikata laifi da cewa jihar za ta zama “wuri mai zafi” gare su. Ya ce gwamnati ba za ta jinkirta daukar mataki ba, kuma duk wanda aka kama zai fuskanci hukunci mai tsauri.

