A ranar Laraba, 19 ga Nuwamba 2025, gwamnatin Sokoto ta bayyana cewa an kammala gina tashar samar da wutar lantarki mai zaman kanta (IPP) da ta shafe shekaru tana jira. Kwamishinan makamashi na jihar, Alhaji Sanusi Danfulani, ya sanar da hakan yayin da ya jagoranci manema labarai a duba aikin, inda ya ce kwararru sun tabbatar da cewa aikin ya kai matakin gamsarwa.
Danfulani ya bayyana cewa gwamnati ta zuba biliyoyi a aikin, ciki har da N1.5bn da Gwamna Ahmed Aliyu ya bayar domin kammalawa da gyaran wasu sassa. Haka kuma ya gode wa tsohon gwamna kuma jagoran APC a jihar, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko, wanda ya fara aikin tun 2008. Ya ce kwamitin fasaha zai sake zama da kwangilar don tsara mataki na gaba.
A zantawarsa da Kakaki24 yayin ziyarar, Daraktan Sashen Lantarki na ma’aikatar, Injiniya Abubakar Shehu, ya tabbatar da cewa an gwada wasu manyan kayayyakin injin din makon jiya. Sai dai ya ƙi bayyana yadda wutar za ta rika fita ko yadda za a rarraba ta, yana mai cewa hakan ya rage wa hukumomin wutar lantarki da gwamnatin jihar.
Aikin IPP ɗin mai karfin megawatt 38 an fara shi a 2008 kan farashin N3.8bn tare da alkawarin kammalawa cikin watanni shida, amma ya dinga samun jinkiri daga 2009 zuwa 2019. Daga baya gwamnatin Tambuwal ta zuba karin N1.7bn a 2020, sannan gwamnatin yanzu ta yi ƙarin N1.5bn har aikin ya kammala.

