Gwamnatin Tarayya ta kashe jimillar Naira Tiriliyan 1.98 a matsayin tallafin wutar lantarki cikin watanni 12, daga Oktoban 2024 zuwa Satumbar 2025, duk da matsin da take fuskanta na biyan bashin sama da naira tiriliyan 4 da ake bin ta ga kamfanonin samar da wuta.
Rahotannin Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Ƙasa (NERC) sun nuna cewa rashin daidaiton kuɗin wuta da farashin kasuwa ya sa gwamnati ke ci gaba da ɗaukar gibin farashi, inda a zango na uku na 2025 kaɗai aka kashe naira biliyan 458.75 a matsayin tallafi.
Masana da ƙungiyoyin masu amfani da wuta sun bayyana cewa tsarin tallafin bai dore ba, suna masu cewa duk da ƙarin kuɗin Band A, har yanzu ana fama da asarar kuɗi, satar wuta da ƙarancin biyan kuɗaɗe daga kamfanonin rarraba wuta, lamarin da ke ci gaba da raunana ɓangaren lantarki na ƙasar.

