Gwamnatin Tarayya ta nuna damuwa game da yadda wasu mutane ke lalata aikin gina babban titin Abuja–Kaduna–Kano da ake ci gaba da yi. Karamin Minista na Ma’aikatar Ayyuka, Bello Muhammad Goronyo, ya bayyana haka yayin duba aikin a ranar Asabar, inda ya ce an samu rahotanni na wasu bata-gari da ke balle ƙarafa da sauran kayan aikin titi domin sayarwa.
Goronyo ya bayyana cewa an ga misali a kusa da gadar Jaji a Kaduna, inda wasu masu sayen shara da ake kira Baba Bola suka kwashe sandunan ƙarfe daga sabbinn gadoji. Haka kuma, akwai wasu da ke amfani da sabon titin wajen busar da hatsi ko zubar da shara, da ma yin ramuka domin saka igiyoyin wutar lantarki ko ruwa.
Ministan ya yi kira ga shugabannin al’ummomi da su fadakar da jama’arsu su daina irin waɗannan ayyuka da ke durƙusar da ci gaban aikin da gwamnati ta zuba kuɗi mai yawa a kan sa. Ya ce titin na da muhimmanci wajen rage lokacin tafiya, kara tsaron hanya da rage haɗura. Haka kuma, ya bayyana cewa tun fara aikin, matsalolin tsaro a hanyar suka ragu sosai.
A nasa ɓangaren, Daraktan Hanyoyi na Ma’aikatar Ayyuka, Clement Ogbuagu, ya ce aikin na tafiya bisa tsari, inda ya tabbatar da cewa gwamnati da kamfanin mai aikin ba sa gajiya wajen tabbatar da kammala titin cikin lokaci. Ya bayyana aikin a matsayin ɗaya daga cikin manyan ayyukan hanya da ke tafiya da sauri a ƙasar.

