Hukumar Kiyaye Haddura ta Ƙasa (FRSC) a jihar Bauchi ta tabbatar da mutuwar fasinjoji 9, yayin da mutane 10 suka jikkata sakamakon wani mummunan haɗarin mota da ya faru a jihar.
Kwamandan sashen FRSC na jihar, CC Apaji Danladi Boyi, ya ce lamarin ya faru da misalin 6:20 na safe a kan hanyar Jama’are–Azare a titin Kano–Maiduguri, inda motar kasuwanci mai lambar KTG 181 ZZ ke dauke da fasinjoji 19 daga Gombe zuwa Kano.
Binciken farko ya nuna cewa gudu fiye da kima, gajiya da rasa ikon sarrafa mota ne suka haddasa hatsarin. Jami’an FRSC sun kai wadanda suka jikkata Asibitin Koyarwa na Tarayya, Azare, yayin da aka ajiye gawarwakin mamatan a dakin ajiyar gawa domin tantancewa da mika su ga iyalansu.

