Wasu Sanatoci a Majalisar Dattawan Najeriya sun nuna damuwa kan umarnin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na janye jami’an ’yan sanda da ke tsaron manyan mutane (VIPs), inda suka ce matakin na iya barin su cikin barazana ta tsaro a lokacin da hare-hare da garkuwa da mutane ke ƙaruwa a faɗin ƙasar. A zaman su na ranar Laraba26 ga Nuwamba, Sanatoci da dama sun bayyana cewa su ne manyan abubuwan da ’yan bindiga da ’yan ta’adda ke nema, don haka janye musu tsaro a wannan lokaci ba dai-dai ba ne. Sun kuma ce su kan yi zirga-zirga zuwa yankuna masu hadari a lokacin gudanar da ayyukan mazabu da sa ido, abin da ke kara musu bukatar tsaro.
Rahoton ya ce tattaunawar ta samo asali ne daga maganar da Sanata Oyelola Ashiru kan bukatar gaggawar shirin gwamnatin tarayya don dakile matsalar tsaro da ke kara ta’azzara. Sanatoci da dama ciki har da Aliyu Wamakko da Tahir Monguno sun bayyana cewa janye tsaro zai kara bude kofar hare-hare, yayin da wasu suka nemi a sake duba tsarin saboda matsayin kasar a halin yanzu. A sakamakon haka, Majalisar Dattawa ta amince da tattaunawa da Shugaban Kasa da hukumomin ’yan sanda don neman a gyara ko sassauta tsarin.
Majalisar ta kuma tattauna batun dokar yaki da garkuwa da mutane, inda ta amince cewa a daidaita ta ta yadda satar mutane za ta zama laifin ta’addanci tare da hukuncin kisa idan an sabunta dokar. Sanatoci sun yi nuni da cewa ’yan bindiga na kara samun karfin gwiwa, yayin da wasu suka bukaci a hana tattaunawa ko biyan kudin fansa ga masu garkuwa da mutane. Har ila yau, Majalisar ta bukaci a kafa rundunar haɗin gwiwa a yankin Kwara–Kogi da kuma gudanar da bincike kan janye sojoji a Kebbi kafin sace dalibai.
A wani bangare, Majalisar ta tattauna yiwuwar sake duba dokar mallakar bindiga domin bai wa ’yan kasa masu kwarewa damar mallakar kayan kariya. Mataimakin Shugaban Majalisar, Barau Jibrin, ya ce gwamnatocin jihohi dole su kara hadin kai da hukumomin tsaro na tarayya domin magance matsalar tsaro. Ya kara da cewa Shugaba Tinubu na daukar matakai, amma ana bukatar karin jari, kayan aiki da inganta rundunar ’yan sanda fiye da canza suna. Ana sa ran Majalisar za ta mika sakamakon tattaunawar ga Shugaban Kasa tare da samun martani cikin mako guda.

