Ministan Harkokin Waje na Najeriya, Yusuf Tuggar, ya bayyana cewa dangantakar Najeriya da Jamus na ƙara ƙarfi, inda yanzu haka fiye da kamfanoni 90 na ƙasar Jamus ke gudanar da harkokinsu a Najeriya. Ya bayyana hakan ne a lokacin bikin tunawa da Ranar Haɗewar Jamus da aka gudanar a birnin Abuja, inda ya ce kamfanonin suna taimakawa wajen samar da ayyukan yi da musayar fasaha, tare da tabbatar da Jamus a matsayin ƙasashen da ke sahun gaba wajen kasuwanci da Najeriya.
Tuggar, wanda Babban Jami’in Ma’aikatar Harkokin Waje, Wahab Akande, ya wakilta, ya jaddada cewa Jamus ta kasance abokiyar hulɗa mai ƙima wacce ke da gagarumar rawar da take takawa wajen bunkasa tattalin arzikin Najeriya. Ya ce dangantakar kasashen biyu ta samu ci gaba sosai musamman a fannin kasuwanci da kirkire-kirkire.
A nasa bangare, Konsul Janar na Jamus dake Lagos, Daniel Krull, ya tabbatar da aniyar ƙasarsa ta zurfafa haɗin gwiwa da Najeriya a fannoni daban-daban ciki har da kasuwanci, fina-finai, kimiyya da makamashi. Ya ce suna ƙoƙarin faɗaɗa sashen bayar da biza domin sauƙaƙa wa masu neman tafiya Jamus, tare da ƙirƙirar sabbin haɗin gwiwa a fannin fasaha da masana’antar nishadi.
Krull ya bayyana cewa Jamus na ɗaya daga cikin manyan abokan kasuwancin Najeriya a yankin Afirka ta Yamma, inda kawai Afirka ta Kudu ke gaban Najeriya wajen musayar kaya da Jamus. Ya ƙara da cewa zuwan wakilan kamfanonin fina-finai na Jamus zuwa taron Africa International Film Festival (AFRIFF) a Lagos, wata alama ce ta yadda haɗin gwiwar al’adun kasashen biyu ke ƙara ƙarfi da fatan amfanar masana’antar fina-finan Najeriya.

