Kotun Tarayya da ke Abuja ta ƙi amincewa da bayar da beli ga Kwamishinan Kuɗin Jihar Bauchi, Yakubu Adamu, da wasu mutum uku da ake tuhuma da laifin tallafa wa ta’addanci da safarar kuɗi. Alkalin kotun, Justice Emeka Nwite ne ya yanke hukuncin.
Sauran waɗanda ake tuhuma a shari’ar sun haɗa da Balarabe Ilelah, Bose Aminu da Kabiru Mohammed, waɗanda ake zargin da aikata laifuka 10 da suka shafi karɓar kuɗi ba ta tsarin banki ba. EFCC ta ce Adamu ya karɓi kuɗaɗen da suka kai dala miliyan 6.95 a shekarar 2024, abin da doka ta haramta.
A hukuncinsa, alkalin kotun ya ce laifukan na da barazana ga tsaro da zaman lafiya, don haka adalci ya fi buƙatar hanzarta shari’ar maimakon bayar da beli. Kotun ta umarci a ci gaba da sauraron shari’ar cikin gaggawa, yayin da EFCC ta musanta zargin cewa ana bin shari’ar ne da dalilan siyasa.

