Wata Babbar Kotu da ke zamanta a Babban Birnin Tarayya Abuja, a ranar Alhamis 18 ga Disamba, 2025, ta ƙi amincewa da buƙatar beli da tsohon Antoni Janar kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, ya gabatar domin a sake shi daga tsarewar Hukumar EFCC. Mai shari’a Babangida Hassan ya ce ba zai iya ba shi beli ba, ganin cewa wata kotu mai matsayi ɗaya ta riga ta ba EFCC umarnin tsare shi domin ci gaba da bincike.
Malami, wanda ke daga cikin manyan jiga-jigan haɗakar ’yan adawa tare da neman takarar gwamna a Jihar Kebbi, yana tsare a hannun EFCC tun daga Litinin na makon da ya gabata bisa zargin karkatar da kuɗaɗen gwamnati. Lauyansa, Sulaiman Hassan (SAN), ya nemi kotu ta ba shi beli, yana mai cewa tsarewar da ake yi masa ba bisa ƙa’ida ba ce.
Sai dai lauyan EFCC, Jibrin Okutepa (SAN), ya shaida wa kotu cewa hukumar na tsare Malami ne bisa sahihin umarnin tsarewa da Babbar Kotun FCT ƙarƙashin Mai shari’a S. C. Oriji ta bayar. A hukuncinsa, Mai shari’a Hassan ya jaddada cewa dokar ACJA ta amince da irin wannan tsarewa, yana mai cewa amincewa da buƙatar belin zai zama kamar kotun na ƙalubalantar hukuncin wata kotu mai matsayi ɗaya, abin da doka ba ta ba shi ikon yi ba.

