Jagoran jam’iyyar NNPP na ƙasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya taya Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, murnar cika shekara 63 a duniya. Kwankwaso ya bayyana hakan ne cikin saƙon taya murna da ya fitar a ranar Litinin, 5 ga Janairu, 2026.
A cikin saƙon, Kwankwaso ya tuno da doguwar alakar siyasa da ke tsakaninsa da Yusuf, inda ya ce gwamnan ya taɓa yi masa aiki a muƙamai daban-daban. Ya ce Yusuf ya fara ne a matsayin Mataimaki na Musamman, daga bisani Babban Mataimaki na Sirri, sannan ya Kwamishina a wa’adinsa na biyu kafin kuma ya zama gwamnan Kano.
Kwankwaso ya bayyana cewa gudunmawar da Yusuf ya bayar a waɗannan muƙamai ta taimaka matuƙa wajen aiwatar da tsare-tsare da shirye-shiryen ci gaban jihar Kano. Ya kuma yi masa fatan samun lafiya, hikima da nasara yayin da yake ci gaba da jagorantar al’ummar jihar.

