Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS) ta kama kwantena 20 da aka karkatar da su daga hanyoyin da aka tanada, masu kimar Naira miliyan 769.5, a jihohin Kano da Jigawa cikin zangon na biyu da na huɗu na shekarar 2025. Babban Kwanturola-Janar na Kwastam, Bashir Adewale Adeniyi, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da ya gudanar a hedkwatar rundunar Kano/Jigawa a Jumma’a, 19 ga Disamba, 2025.
A cewar Adeniyi, an kama kwantenan ne sakamakon ƙarfafa matakan sa ido don dakile juya kayan da ya kamata su je tashoshin cikin ƙasa da yankunan ciniki na musamman (Free Trade Zones), yana mai bayyana hakan a matsayin karya doka mai tsanani a ƙarƙashin Dokar Kwastam ta 2023. Ya ce juya kaya na janyo asarar kuɗaɗen shiga, rashin adalci a kasuwanci, da kuma barazana ga tsaro da martabar Najeriya a idon duniya.
Ya bayyana cewa an kama kwantenan a wurare daban-daban da suka haɗa da Hadejia Road, Dakata Industrial Area, Kwari Market da APM Terminal Kano, ciki har da tayil, man dizal, yadudduka, tsofaffin kaya da kayan aikin lafiya. Bechi Hausa ta ruwaito cewa an riga an yanke wa wani mai suna Abdulrahman Sani Adam hukuncin daurin shekaru uku ko tara Naira miliyan 3, yayin da Kwastam ke shirin faɗaɗa amfani da na’urar bibiyar kwantena ta lantarki a faɗin ƙasa domin hana irin wannan laifi a nan gaba.

