Majalisar Dattawa ta tabbatar da nadin Dr. Bernard Doro a matsayin sabon minista bayan wani gajeren zaman tantancewa da bai wuce mintuna talatin ba a yau Alhamis 30 ga Oktoba a Abuja. Taron tantancewar ya samu halartar shugaban jam’iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Goshwe Yilwatda, wanda shi ma tsohon ministan harkokin jin kai da rage talauci ne.
Dr. Doro, wanda shi ne minista na uku daga jihar Filato a wannan gwamnati, ya bayyana burinsa na kafa tsarin taimakon jin kai da ya dogara da gaskiya, adalci da cin gashin kai. Sanatoci sun yaba da kwarewarsa da gogewarsa wajen gudanar da aiki, inda suka amince da nadinsa bayan ya amsa tambayoyi kadan.
Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya karanta wasikar da Shugaba Bola Tinubu ya aikowa majalisar, inda ya nemi a tabbatar da Doro bisa sashe na 147, sakin layi na 2 na Kundin Tsarin Mulki na 1999 (da aka yi wa kwaskwarima).
Nadin Dr. Doro ya biyo bayan nada Farfesa Yilwatda a matsayin sabon shugaban jam’iyyar APC a watan Yuli, wanda ya bar kujerarsa ta minista. Wannan tabbatarwa na nufin cewa gwamnatin Tinubu na ci gaba da cike guraben manyan mukamai domin tabbatar da daidaito da ingantaccen tsarin gudanar da mulki.

