Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa matsin tattalin arzikin da ake fuskanta yanzu zai zama tarihi nan ba da jimawa ba, domin kasar na shiga sabon mataki na ci gaba. Ya bayyana haka ne a wajen taron Nigeria Renewable Energy Innovation Forum (NREIF) da aka gudanar a Abuja ranar Talata. Shettima ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu na tare da al’umma, yana kuma jin radadin halin da ake ciki.
Shettima ya bayyana cewa taron yana da nufin jawo hankalin masu zuba jari domin kafa cibiyar kera kayayyakin makamashin sabuntawa a Najeriya. Ya ce akwai damar zuba jari fiye da dala biliyan 410 a tsakanin yanzu da shekarar 2060 domin bunkasa bangaren makamashi da kuma tabbatar da samun wutar lantarki ga miliyoyin al’ummar da ke fama da talaucin makamashi. Ya kara da cewa manufar gwamnati ita ce samar da tsarin wutar lantarki mai karfin 277 gigawatts nan da shekarar 2060.
Mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa an riga an samu alkawarin zuba jari sama da dala miliyan 400 a ɓangaren masana’antar makamashin sabuntawa, ciki har da kera solar panels, na’urorin auna wuta na zamani, da kuma ajiyar batir. Wannan, a cewarsa, zai samar da fiye da ayyuka 1,500 kai tsaye a jihohi daban-daban, tare da karfafa gwiwar duniya kan shirin Najeriya na zama cibiyar masana’antar makamashin tsabta a Afirka.
A nasa jawabin, Ministan Wuta Adebayo Adelabu ya ce taron NRIP 2025 ba kawai wani taro ba ne, illa dai sanar da shirye-shiryen Najeriya na jagorantar juyin juya halin makamashin sabuntawa a nahiyar Afirka. Ya jaddada cewa manufar “Nigeria First Policy” ta kunshi alfahari da kasa, bunkasa masana’antu, da tabbatar da dorewar tattalin arziki — inda sabbin fasahohin makamashi za su kasance da tambarin “Made in Nigeria.”

