Ministan Kuɗi kuma Ministan Tsare-tsaren Tattalin Arziki na Ƙasa, Mista Wale Edun, ya tafi ƙasar Birtaniya domin samun kulawar likitoci, bayan ya yi rashin lafiya a kwanakin baya. Majiyoyi da dama daga fadar gwamnati sun tabbatar da hakan da safiyar Talata, inda suka bayyana cewa ministan ya bar Abuja zuwa Legas da daddare, daga nan kuma ya wuce Landan ta jirgin British Airways.
Tun a ranar Lahadi, wasu jami’an gwamnati sun bayyana cewa Edun na karɓar magani a gidansa a Abuja karkashin kulawar likitocin Najeriya, suna mai ƙaryata jita-jitar cewa ya kamu da ciwon bugun jini. Sai dai daga baya, likitoci sun ba da shawarar a kai shi ƙasashen waje don ci gaba da jinya, wanda aka aiwatar a yanzu.
Wani babban jami’in gwamnati ya tabbatar da cewa Edun na fama da rashin lafiya mai ɗan tsanani amma ba ciwon da zai hana shi aiki gaba ɗaya ba. Haka kuma, mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin labarai, Bayo Onanuga, ya tabbatar da cewa Edun ba zai iya halartar taron shekara-shekara na Bankin Duniya da IMF da ke Washington, D.C. ba. Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Olayemi Cardoso, ne zai jagoranci tawagar ƙasar.
Edun, wanda aka naɗa a watan Agustan 2023, ya taka muhimmiyar rawa wajen aiwatar da manufofin tattalin arzikin gwamnatin Tinubu, ciki har da cire tallafin mai da daidaita farashin musayar kuɗi. Har yanzu Ma’aikatar Kuɗi ba ta fitar da wata sanarwa ta hukuma kan halin da ministan ke ciki ba.

