Sakataren Yaƙin Amurka, Pete Hegseth, ya bayyana cewa ma’aikatarsa tana shirin kai hari a Najeriya, sakamakon zarge-zargen kisan Kiristoci da ake cewa na ƙaruwa a ƙasar. Hegseth ya fadi haka ne bayan shugaban Amurka, Donald Trump, ya wallafa a Truth Social cewa gwamnatin Najeriya “na rufe ido” kan hare-haren da ake kaiwa Kiristoci, yana mai gargadi cewa Amurka na iya katse tallafi da kuma kaddamar da farmaki kan kungiyoyin ta’addanci a Najeriya.
Trump ya ce idan gwamnati ta gaza kare Kiristoci, Amurka za ta “tsinke duk wata taimako ga Najeriya” kuma tana iya shiga ƙasar “da makamai a bude” domin kawar da ‘yan ta’adda. Ya kuma umarci Ma’aikatar Yaƙi ta fara shirin kai farmaki, yana mai cewa, “idan muka kai hari, zai kasance da sauri, da ƙarfi, kuma da daɗi — kamar yadda ‘yan ta’addan ke kai wa Kiristoci hari.”
A martanin da Hegseth ya wallafa a dandalin X (Twitter), ya tabbatar da cewa sun fara shiri bisa umarnin shugaban ƙasarsu. Ya ce, “Gobarar kashe Kiristoci ba za ta ci gaba ba. Idan gwamnatin Najeriya ba ta kare su ba, mu ne za mu kare su ta hanyar kawar da ‘yan ta’addan da ke aikata waɗannan manyan laifuka.” Wannan ya nuna yiwuwar Amurka ta ɗauki matakin soja kai tsaye idan halin da ake ciki bai sauya ba.
Wannan lamari ya faru ne kwana guda bayan Trump ya sake sanya Najeriya cikin jerin ƙasashen da ke da “tsananin take hakkin addini,” yana zargin cewa ana kashe Kiristoci da yawa a hannun kungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi. Sai dai shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya mayar da martani cikin ƙarfi, yana cewa Najeriya ƙasa ce mai dimokuraɗiyya da ke ba kowa ‘yancin addini, kuma gwamnatin sa ba za ta yarda wani ya bata sunan ƙasar da ƙarya ba.

