Majalisar Dokokin Jihar Rivers ta bayyana cewa tsarin tsige Gwamna Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa Farfesa Ngozi Odu na ci gaba da gudana, sabanin jita-jitar da ke yawo cewa an dakatar da shi. Majalisar ta ce an fara matakin ne tun Alhamis, 8 ga Janairu, 2026.
A cikin wata sanarwa da Enemi George, shugaban kwamitin yada labarai na majalisar ya sanya wa hannu, an ce an bi dukkan ka’idojin kundin tsarin mulkin kasa. Sanarwar ta kara da cewa Kakakin Majalisar, Martins Amaewhule, ya riga ya mika wa gwamnan da mataimakiyarsa takardun tuhumar aikata manyan laifuka, ana jiran martaninsu.
Majalisar ta kuma zargi wasu mutane da kafafen yada labarai da yada labaran karya domin rikita al’umma, tana mai cewa ba za ta ja da baya ba wajen kare doka da oda. Ta gode wa al’ummar jihar Rivers bisa goyon baya da addu’o’i, tana jaddada kudirinta na sauke nauyin da kundin tsarin mulki ya dora mata.

