Wata babbar kotu da ke Abuja ta yanke wa Hussaini Isma’ila, wanda aka fi sani da Maitangaran, hukuncin zama a gidan yari na tsawon shekara 20, kan zargin kitsa kai hare-haren ta’addanci a Kano da sauran sassa a shekarun baya. Mai shari’a Emeka Nwite ne ya yanke hukuncin, bayan ya same shi da laifuka daban-daban da suka shafi ta’addanci da hallaka rayuka.
Kotun ta tabbatar da cewa Maitangaran, wani babban jami’i a cikin kungiyar ISWAP, ya jagoranci kai hari a shelkwatar rundunar ‘yan sandan Kano da ke Bompai, tare da wasu hare-hare a Kabuga, Unguwa Uku, Kasuwar Waya da Farm Centre a shekarar 2012, lamarin da ya kashe mutane da dama tare da jikkata wasu. Hukumar DSS ce ta gurfanar da shi, tana mai gabatar da shaidu guda biyar da suka tabbatar da rawar da ya taka a kai hare-haren.
A yayin ci gaba da shari’ar—wanda tun farko ya musanta laifukan—Maitangaran daga bisani ya amince da zarge-zargen, inda lauyansa ya roƙi sassauci, yana mai cewa wanda yake karewa ya nuna nadama domin hana bata wa kotu lokaci. Wannan lamari ya kasance muhimmin abin lura a shari’ar da ta sha jinkiri tun bayan kama shi a 31 ga Agusta 2017 a Tsamiya Babba, ƙaramar hukumar Gezawa a Kano.
Bechi Hausa News ta gano cewa bayan yanke hukuncin, mai shari’a ya umurci hukumar kula da gidajen yari ta Najeriya da ta ajiye shi a duk gidan yari da ta ga dama, tare da sanya shi cikin shirin gyaran hali da canza akida, domin farfado da tunaninsa daga tasirin kungiyoyin ta’addanci.

