Shugaban ƙasar Kamaru, Paul Biya, ya sake lashe zaben shugaban ƙasa karo na takwas, kamar yadda Majalisar Kundin Tsarin Mulki ta ƙasar ta tabbatar. Biya, mai shekara 92, ya samu nasara da kashi 53.66% na ƙuri’un da aka kaɗa, yayin da jagoran adawa Issa Tchiroma Bakary ya biyo baya da kashi 35.19%. Wannan sakamako na nufin Biya zai ci gaba da mulkin ƙasar har zuwa shekara ta 2032.
Biya, wanda ya hau mulki tun daga 1982, ya zama ɗaya daga cikin shugabannin da suka fi daɗewa kan mulki a nahiyar Afirka. Duk da tsananin shekaru da kalubalen da ƙasar ke fuskanta, shugaban ya ci gaba da samun goyon bayan manyan jam’iyyu da sassan tsaron ƙasa, abin da ya taimaka masa wajen sake samun nasara a wannan zaɓen.
Sai dai jam’iyyar adawa ta nuna rashin gamsuwa da sakamakon, tana zargin cewa an samu kura-kurai a tsarin gudanar da zaɓen. Duk da wannan, hukumomin zaɓe sun bayyana cewa an gudanar da zaɓen cikin kwanciyar hankali da bin ƙa’ida, tare da yabon ƙasashen ketare da suka sa ido a kan zabukan.

