Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Jigawa ta samu nasarar kama mutane 153 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban, tare da kwace dubban kwayoyi da kuɗi da babur, a wani samame da aka kai cikin jihar. Kakakin rundunar, SP Shi’isu Adam, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a Dutse, babban birnin jihar, a ranar Litinin 06 ga Oktoba, 2025.
An gudanar da samamen ne a dukkanin sassan rundunar 42 da ke jihar, inda aka kai farmaki maboyar ‘yan ta’adda, wuraren shaye-shaye da wuraren sayar da miyagun kwayoyi, a wani yunkuri na dakile laifuka. Daga cikin kayan da aka kwace akwai fiye da kwayoyi 3,000 na Exol, D5 da Tramadol, ganja a manyan fakiti da wraps 943, wasu haramtattun magunguna, sirup, da kuɗi N228,570, da kuma babur ɗaya.
An gurfanar da dukkan waɗanda aka kama a gaban kotu bayan kammala bincike, yayin da rundunar ta ce wannan samame na nuna jajircewarta wajen yaki da miyagun kwayoyi da aikata laifi. Rundunar ta kuma yi kira ga jama’a da su rika kai rahoton duk wani motsi da suke zargi, tare da tabbatar da sirri da ɗaukar mataki cikin gaggawa.
Rundunar ‘yan sanda ta Jigawa ta sha alwashin ci gaba da gudanar da irin waɗannan matakai har sai an kawar da laifuka da safarar kwayoyi a jihar. Ta kuma gargadi masu aikata laifi da su daina, in ba haka ba za su fuskanci hukunci mai tsanani.

