A wani mataki na gaggawa domin shawo kan matsalar garkuwa da mutane da ke ƙara kamari, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya umarci a janye kusan ’yan sanda 100,000 daga jikin manyan mutane (VIPs) domin maida su aikin tsaro na jama’a da ya haɗa da yaƙi da ’yan ta’adda.
A ganawar tsaro da aka gudanar a Abuja ranar Lahadi tare da Shugabannin Rundunonin Tsaro da Daraktan DSS, Tinubu ya bayar da umarnin cewa daga yanzu NSCDC za ta riƙe tsaron VIPs, yayin da ’yan sanda za su koma filin aiki kai tsaye don ƙara cike gibi a yankuna da dama da ke fama da ƙarancin jami’an tsaro. Rahotanni sun nuna cewa Najeriya na da ’yan sanda 371,800 kacal, kuma rabinsu suna bauta wa VIPs maimakon al’umma.
A cewar mai ba Shugaban Kasa shawara kan labarai, Bayo Onanuga, gwamnati ta kuma amince da daukar sabbin ’yan sanda 30,000 tare da hadin gwiwar jihohi domin inganta cibiyoyin horaswa. Wannan na zuwa ne bayan fargabar da ta taso kan yadda sojoji suka janye daga makarantar St. Mary a Papiri kafin a yi garkuwa da ɗalibai fiye da 300. Rundunar Soji ta ce tana bincike kan dalilin janyewar.
A halin da ake ciki, rundunar Operation Fansan Yamma ta umurci sojoji da su matsa lamba domin ceto ɗalibai, inda kwamandojin rundunar suka kai ziyara Papiri tare da tabbatar wa al’umma cewa “’yan bindiga ba za su samu mafaka ba.” Al’ummar yankin sun ce zuwan manyan hafsoshin ya saka musu kwarin gwiwa.
A bangaren siyasa, jam’iyyar APC ta yi zargin cewa tashin hankulan Arewa “na da kamannin shiri na wasu ɓarayi” domin tada hankalin kasa kafin 2027. Wasu jiga-jigan jam’iyyar sun bukaci gwamnati ta bankado masu kutse a cikin tsarin tsaro. A gefe guda kuma, Vatican ta yi kira ga sakin daliban da aka sace, yayin da gwamnoni da dama suka rufe makarantu domin takaita barna — lamarin da masana tsaro suka ce na iya ƙara karfafa masu laifi.
A ranar Lahadi, kusan dalibai 50 daga cikin wadanda aka sace a Papiri sun tsere sun koma gidajensu, amma har yanzu 253 suna hannun ’yan ta’adda tare da ma’aikata 12. Haka kuma, a Kwara, dukkan worshippers 38 da aka sace daga cocin CAC Eruku sun samu ‘yanci bayan wani gagarumin aikin hadin gwiwa da ya samu kulawar Tinubu kai tsaye. gwamnoni da hukumomin tsaro na ƙara haɗa kai domin kare makarantu da al’ummomi yayin da hare-haren ’yan bindiga ke ƙaruwa.

