Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya umarci Hukumar Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON) da ta sake rage kuɗin aikin Hajjin shekarar 2026 nan da kwanaki biyu. Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ne ya isar da wannan umarni yayin wani taro a Fadar Shugaban Ƙasa da shugabannin NAHCON.
Gwamnati ta ce sabon farashin ya zama dole ne saboda darajar naira tana ƙaruwa, kuma akwai buƙatar amfani da farashin canji na yanzu don rage yawan kuɗi kan maniyyata. A bara, maniyyata sun biya tsakanin Naira miliyan 8.5 zuwa 8.6 saboda tsadar Dala.
NAHCON ta bayyana cewa matakin zai ƙara yawan maniyyata saboda sauƙin farashi, yayin da shugabannin hukumar Alhazai na jihohi suka yaba da umarnin shugaban ƙasa, suna mai cewa zai taimaka wa Musulmi da dama su samu damar gudanar da aikin Hajji cikin sauƙi.

