ranar Talata, 2 ga Disamba 2025, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya mika sunan Janar Christopher Gwabin Musa ga Majalisar Dattawa domin tabbatarwa a matsayin sabon Ministan Tsaro. Wannan na zuwa ne bayan murabus ɗin Alhaji Mohammed Badaru Abubakar wanda ya ajiye aiki a ranar Litinin saboda dalilan lafiya.
Janar Musa, wanda zai cika shekara 58 a ranar 25 ga Disamba, tsohon Babban Hafsan Tsaro ne daga 2023 zuwa Oktoba 2025. Yayi manyan ayyuka a rundunar sojin ƙasa, tare da lashe lambar yabo ta Colin Powell Award for Soldiering a 2012. Dan asalin Sokoto ne, ya yi karatunsa a Sokoto da Zariya kafin ya shiga NDA a 1986.
A cikin aikinsa, Janar Musa ya shugabanci sassa daban-daban na soji, ciki har da Operation Lafiya Dole da Multinational Joint Task Force a yankin Tafkin Chadi. Kakaki24 ta tattaro cewa ya taka rawar gani a Operation Hadin Kai, sannan daga baya ya zama kwamandan Infantry Corps kafin nadinsa matsayin CDS a 2023.
A wasikar da ya aika wa Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, Shugaba Tinubu ya bayyana cikakken amincewarsa da kwarewar Janar Musa wajen karfafa tsarin tsaron Najeriya. Yanzu ana jira matakin Majalisar Dattawa kan tabbatar da nadin nasa.

