Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai gabatar da daftarin kasafin kuɗin shekarar 2026 gaban zaman haɗin gwiwa na Majalisar Ƙasa a ranar Jumma’a, 19 ga Disamba 2025, da ƙarfe 2:00 na rana. Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da ofishin Magatakardar Majalisar Ƙasa ya fitar, inda aka umarci duk masu izini da su kasance a wuraren aikinsu tun daga ƙarfe 11:00 na safe, saboda tsaurara matakan tsaro a cikin harabar majalisar.
Kasafin kuɗin 2026 an kiyasta shi ne a kan Naira tiriliyan 54.4, kamar yadda kundin Tsarin Kuɗaɗen Matsakaicin Lokaci (MTEF) da Takardar Tsarin Kasafi (FSP) na 2026–2028 suka nuna. A gefe guda kuma, shugaban ƙasar ya aika da buƙata ga Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai na soke tare da sake zartar da kasafin kuɗin 2024, wanda adadinsa ya kai Naira tiriliyan 43.56, domin kauce wa tafiyar da kasafi fiye da ɗaya a lokaci guda da kuma ƙarfafa aiwatar da manyan ayyukan raya ƙasa.
Rahoton Bechi Hausa ya nuna cewa masana tattalin arziki na nuna ra’ayoyi mabambanta kan matakin, inda wasu ke cewa zai kawo tsari da gaskiya, yayin da wasu ke gargaɗin yiwuwar rikice-rikice da maimaita kasafi. Shugaban Cibiyar CPPE, Dr. Muda Yusuf, ya bukaci a yi cikakken garambawul ga tsarin kasafin ƙasar, yana mai cewa daidaita kashe kuɗi da ainihin kuɗaɗen shiga da kuma rage nauyin biyan basussuka na da matuƙar muhimmanci wajen dawo da amincewa da tattalin arzikin Najeriya.

