Fitaccen likitan nan, Chinonso Egemba, wanda aka fi sani da Aproko Doctor, ya yi gargaɗi ga masu amfani da wayar hannu yayin zama a bayan gida, yana mai cewa irin wannan dabi’a na iya janyo matsalar haemorrhoids.
A cewarsa, zama na dogon lokaci a bayan gida, musamman ana lilo da duba shafukan sada zumunta, yana ƙara matsa lamba ga jijiyoyin jini na ƙasan dubura, wanda ke haifar da kumburi da zafi. Ya ce, “Jikin ɗan Adam an halitta shi ne ya yi abin da zai yi ya tashi, ba wai ya zauna mintuna 30 yana kallo da wayar hannu ba.”
Likitan ya ƙara da cewa zama fiye da mintuna 10 a bayan gida na iya haifar da tara jini a jijiyoyin dubura, wanda daga bisani zai iya haifar da kaikayi, zafi, ko ma zubar jini. Ya yi nuni da cewa mutane su guji matsa ƙashi da ƙarfi domin hakan ma na ƙara tsananta matsalar.
A ƙarshe, Aproko Doctor ya shawarci jama’a su yawaita cin abinci mai ɗauke da sinadarin fibre kamar kayan lambu da ‘ya’yan itatuwa, tare da shan ruwa mai yawa domin sauƙaƙa bayan gida. Wani bincike ma daga Medscape ya tabbatar da cewa mutanen da ke amfani da wayar hannu a bayan gida suna da yuwuwar samun matsala da kaso 46 cikin 100 fiye da waɗanda ba sa yin hakan.

