Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi gargaɗi ga Iran cewa za ta fuskanci mummunan sakamako idan aka ci gaba da kashe masu zanga-zanga a ƙasar. Wannan gargadin ya zo ne a daidai lokacin da zanga-zangar tsadar rayuwa ke ci gaba da girgiza Iran, wadda ta shafe sama da mako guda tana gudana. Trump ya bayyana cewa Amurka tana sanya ido sosai kan abin da ke faruwa a Tehran, duk da cewa ba a bayyana takamaiman matakin da za a ɗauka ba.
Gwamnatin Iran ta yi ƙoƙarin kwantar da hankulan jama’a ta hanyar sanar da shirin bai wa ‘yan ƙasar sabon alawus na wata-wata, kimanin dala bakwai, domin rage tasirin matsalar durkushewar tattalin arziki da ta haddasa tarzoma a ƙasar. Sai dai hakan bai hana ci gaba da zanga-zangar ba, yayin da rahotanni ke nuna cewa an samu rikici a wurare da dama. Jama’a na nuna rashin jin daɗinsu kan yanayin rayuwa da hauhawar farashi a kasashen su.
Rahotanni sun bayyana cewa aƙalla mutane 16 ne suka rasa rayukansu tun bayan barkewar zanga-zangar a Iran. Hakan ya jefa ƙasa cikin yanayin tashin hankali, inda ƙasashen duniya ke nuna damuwa kan yadda ake tafiyar da zanga-zangar. Masu lura da harkokin duniya na ci gaba da kira ga Iran da ta bi hanyoyin zaman lafiya wajen sasanta rikicin.

