Gwamnatin Nigeria ta bayyana damuwa kan rikicin da ke ƙaruwa a ƙasashen yankin Gulf, tana mai gargadin cewa hakan na iya shafar zaman lafiyar yankin da ma duniya baki ɗaya. Ta yi kira ga dukkan ɓangarorin da su kwantar da hankali tare da nuna kamewa.
A cikin sanarwar da Ma’aikatar Harkokin wajen ƙasar ta fitar, an buƙaci a kauce wa duk wani mataki da zai ƙara ta’azzara rikicin. Sanarwar ta jaddada muhimmancin fifita tattaunawa da fahimtar juna fiye da faɗa, tare da bin ƙa’idojin United Nations da Yarjejeniyar Geneva.
Gwamnatin ta kuma yi kira da a rage amfani da ƙarfi domin kare rayukan fararen hula da mutunta ikon ƙasashe da iyakokinsu. Ta bayyana goyon bayanta ga duk wani yunƙuri na diflomasiyya da shiga tsakani domin warware rikicin.

