Sarkin Musulmi kuma Shugaban Ƙungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI), Muhammad Sa’ad Abubakar, tare da Ƙungiyar Limaman Katolika ta Najeriya (CBCN), sun nuna damuwa kan yadda matsalar tsaro ke ƙara ta’azzara a wasu sassan ƙasar nan duk da ƙoƙarin da ake yi na yaƙi da garkuwa da mutane, ta’addanci da sauran laifuka.
A saƙonsa na sabuwar shekarar Musulunci, Sarkin Musulmin ya bukaci haɗin gwiwar al’umma, malamai da hukumomin tsaro wajen dawo da zaman lafiya. Haka kuma ya umarci limaman masallatai da su gudanar da addu’o’in Qunootun-Nawazil tare da sadaukar da sallar Juma’a ta ranar 19 ga Yuni domin neman zaman lafiya da tsaron ƙasa.
A nasa bangaren, Mataimakin Shugaban CBCN kuma Archbishop na Legas, Alfred Martins, ya ce ‘yan Najeriya sun gaji da kashe-kashe da garkuwa da mutane. Ya bukaci gwamnatin tarayya da ta ƙara ƙarfafa jami’an tsaro tare da ɗaukar matakan gaggawa domin kawo ƙarshen matsalar tsaron da ke addabar ƙasar.

