Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya bayyana cewa a shirye yake ya rasa ransa wajen kare ƙuri’un da ya samu a zaɓen 2027. Obi ya faɗi hakan ne a wani taron tattaunawa da aka gudanar a Port Harcourt, babban birnin jihar Rivers.
Obi ya buƙaci ’yan Najeriya su tabbatar da cewa ba a maimaita abubuwan da ya kira “rashin daidaito” da aka samu a zaɓen 2023 ba. A wancan zaɓen, INEC ta kasa ɗora sakamakon zaɓe ta hanyar intanet saboda matsalar da aka ce ta samu a tsarin IReV, lamarin da masu sukar hukumar suka zarge ta da amfani da shi wajen tafka magudi.
Ya ce duk masu shirin yin magudi a zaɓen 2027 ba za su yi nasara ba, tare da kira ga magoya bayansa su fito ranar zaɓe su kada ƙuri’unsu. Obi ya ce babu wanda zai sake tsoratar da masu zaɓe ko hana a ƙirga ƙuri’unsu, yana mai cewa a shirye yake ya mutu domin tabbatar da an kare ƙuri’unsu.
A nasa ɓangaren, mataimakin ɗan takarar NDC, Rabiu Kwankwaso, ya yi kira ga masu zaɓe da su guji kuskuren baya wajen zaɓar shugabannin da ba su da ƙwarewar magance matsalolin ƙasar. Ya ce duk da yawan jihohin da APC ke iko da su a yanzu, jam’iyyar za ta iya rasa zaɓen da ke tafe.

