Gwamnatin Jihar Kano ta ayyana Talata, 1 ga Satumba, 2026, a matsayin ranar hutu domin bai wa mazauna jihar damar gudanar da bikin Takutaha.
Bikin Takutaha wata muhimmiyar al’ada ce ta addini da ake gudanarwa duk shekara domin tunawa da zagayowar watan da aka haifi fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW).
Sanarwar hutun ta fito ne daga Ofishin Ma’aikata na Jihar Kano, inda Babban Sakataren ma’aikatar, Alhaji Abba A. Danguguwa, ya sanya wa hannu a madadin Shugabar Ma’aikatan Jihar, Hajiya Bilkisu Maimota.
Sanarwar ta ce hutun ya yi daidai da 19 ga Rabi’ul Awwal, 1448 bayan hijira, inda ta bayyana cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya amince da ayyana ranar. Ta kuma bukaci ma’aikatan gwamnati su yi amfani da ranar wajen addu’o’i da neman gafara.

