Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya sha alwashin sake buɗe iyakokin Najeriya idan ya samu nasarar lashe zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.
Atiku ya bayyana hakan ne a wani faifan bidiyo da jigo a jam’iyyar ADC, Dele Momodu, ya wallafa, inda ya ce sake buɗe iyakokin zai taimaka wajen farfaɗo da harkokin kasuwanci.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya kuma yi alkawarin bunƙasa tashoshin jiragen ruwa da ke yankin kudancin ƙasar, domin ƙarfafa harkokin kasuwanci da kuma samar da ayyukan yi.
Wannan na daga cikin sabbin manufofin da Atiku ke bayyana wa ’yan Najeriya gabanin zaɓen shugaban ƙasa na 2027, yayin da yake neman mayar da hankali kan harkokin tattalin arziƙi da kasuwanci.

