Tsohon mataimakin shugaban ƙasar Najeriya, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa cire tallafin man fetur shi ne babban abin da ya haifar da matsin tattalin arziƙin da ’yan Najeriya ke fuskanta. Ya ce ƙasar ba ta taɓa shiga irin wannan ƙunci da wahala ba kamar yadda ake ciki yanzu.
Atiku ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da BBC, inda ya ce idan ya samu nasarar hawa mulki a 2027, ba zai cire tallafin man fetur gaba ɗaya lokaci guda ba. Ya ce zai fara ne da kyautata rayuwar talakawa, sannan a hankali a dinga cire tallafin.
A ranar 29 ga watan Mayun 2023 ne Shugaba Bola Tinubu ya sanar da cire tallafin man fetur, lamarin da ya haifar da tashin farashin man fetur nan take. Hakan kuma ya shafi fannonin rayuwa daban-daban tare da ƙara tsadar kayan masarufi a ƙasar.
Gwamnatin Najeriya ta mayar wa Atiku martani, tana mai cewa kalamansa sun nuna rashin fahimtar halin tattalin arziƙin ƙasar. Ministan Kuɗi, Taiwo Oyedele, ya ce an tara naira tiriliyan 15.8 daga kuɗaɗen tallafin tsakanin Yunin 2023 da Disamban 2025, inda aka kashe kuɗin wajen raba wa jihohi, ƙarin albashi da alawus, biyan basussuka da manyan ayyuka.

