Malaman addinin Musulunci da shugabannin addini sama da 500 daga jihohi 19 na Arewacin Najeriya da Abuja sun bayyana goyon bayansu ga tazarcen Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027.
Sanarwar Ofishin Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Siyasa, Alhaji Ibrahim Kabir Masari, ta ce malaman sun bayyana matsayar ne yayin taron Northern Muslim Intellectual Forum da aka gudanar ranar Asabar, 22 ga Agusta 2026, a Dutse, Jihar Jigawa.
A taron, mahalarta sun tattauna batutuwan tsaro, tattalin arziki, ababen more rayuwa da ci gaban Arewa. Gwamnonin Jigawa, Kano, Yobe, Sokoto da Kaduna, da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, na cikin wadanda suka halarci taron.
Sanarwar ta ce mahalarta taron, da suka hada da malamai, limamai, mahaddata Alƙur’ani da masu wa’azi, sun bayyana amincewarsu da gwamnatin Tinubu. Sun kuma yi kira ga mutanen Arewa da ’yan Najeriya baki daya su mara masa baya da sauran ’yan takarar APC a zaɓe mai zuwa.

