Gwamnatin Jihar Kano ta yi gargaɗin ɗaukar tsauraran matakai kan duk wanda ya karya dokokin ƙasa ko ya shiga harkar saye da sayar da filaye ba bisa ka’ida ba a yankin Rimin Zakara. Kwamishinan Ƙasa da Tsara Birane, Abduljabbar Muhammad Umar Garko, ne ya bayyana hakan yayin ziyarar gani da ido da ya kai yankin ranar Alhamis 03 ga Satumba, 2026.
Kwamishinan ya ce an kawo ƙarshen doguwar takaddamar da ta kwashe sama da shekaru 50 tsakanin al’ummar Rimin Zakara da Jami’ar Bayero, musamman kan mallakar filaye da iyakokin yankin. Ya ce gwamnatin jihar ta shiga tsakani tare da tabbatar da an yi wa masu haƙƙi adalci.
Garko ya ce duk wanda ya sake yunƙurin gina wani abu ko gudanar da harkar filaye a wuraren da aka tabbatar mallakin Jami’ar Bayero ne, tabbas zai fuskanci hukunci. Ya ƙara da cewa gwamnati ba za ta amince da mamaye ko karya dokokin da suka shafi wuraren da aka ware wa hukumomi da cibiyoyin gwamnati ba.
Jagoran al’ummar Rimin Zakara, Alhaji Baba Habu Mika’il, da wakilin Jami’ar Bayero, Farfesa Ahmad Mahmud Tsauni, sun yaba wa Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, da gwamnatin jihar kan yadda suka shiga tsakani wajen warware rikicin. Sun ce matakin ya taimaka wajen tabbatar da adalci, biyan diyya da samar da mafita da za ta ƙarfafa zaman lafiya da kyakkyawar fahimta tsakanin al’ummar yankin da jami’ar.

