Gwamnatin Tarayya ta ayyana Talata, 25 ga Agusta 2026, a matsayin ranar hutu domin bikin Maulidin Annabi Muhammad SAW.
Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya sanar da hakan a madadin gwamnatin tarayya, cikin wata sanarwa da Babbar Sakatariyar ma’aikatar, Dakta Magdalene Ajani, ta fitar ranar Juma’a.
Ministan ya taya Musulmi a Najeriya da sauran sassan duniya murnar zagayowar Maulidin, inda ya buƙace su da su yi tunani kan koyarwar Annabi Muhammad SAW, musamman tausayawa, tawali’u da hidima ga bil’adama.
Tunji-Ojo ya kuma yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi amfani da lokacin wajen addu’ar samun zaman lafiya, haɗin kai da zaman lafiya tsakanin al’umma, tare da yin bikin cikin natsuwa da mutunta juna.

