Wasu ’yan bindiga sun kai hari a yankin ƙauyen Beli da ke kusa da garin Zarewa a karamar hukumar Rogo ta jihar Kano, inda suka kashe wani almajiri tare da sace shugaban jam’iyyar APC na karamar hukumar, Alhaji Abdullahi Beli.
Rahotanni sun ce maharan sun kutsa ƙauyen Beli ne a daren Litinin, inda suka sace Abdullahi Beli daga gidansa jim kaɗan bayan ya dawo daga wani taron jam’iyya a Zarewa. Harin ya kuma haddasa harbe-harbe da firgici a cikin ƙauyen.
Sakataren yaɗa labarai na APC a jihar Kano, Auwalu Sojo, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa Beli na hannun masu garkuwa da shi, yayin da jami’an tsaro suka fara aikin ceto bayan sanar da su aukuwar lamarin.
A kwanakin baya ma, wasu hare-haren ’yan bindiga a Kano sun yi sanadin mutuwar mutane da dama, ciki har da shugaban APC na mazabar Rantan a karamar hukumar Bebeji, Alhaji Garba Buba, yayin da wasu maharan suka kashe mutum uku tare da jikkata biyar a ƙauyen Chiromawa na karamar hukumar Garun Malam.

