Sarkin Gumel, Alhaji Ahmed Muhammad Sani III, ya rasu yana da shekaru 84 bayan fama da rashin lafiya a ƙasar Masar. Wata majiya daga fadar sarkin ta tabbatar da rasuwar a ranar Alhamis.
Majiyar ta ce fadar za ta fitar da ƙarin bayani kan shirye-shiryen jana’izarsa. An haifi marigayin a ranar 12 ga Disamba, 1942, kuma shi ne sarki na 16 da ya hau kujerar masarautar Gumel.
Kafin ya zama sarki, Ahmed Muhammad Sani III ya yi fice a fannin ilimi da aikin gwamnati. Ya samu Diploma a Public Administration a 1963, sannan ya ƙara samun Higher Diploma a 1970, kafin ya tafi Jami’ar Ohio da ke Amurka inda ya karanci Political Science da International Relations, ya kammala a 1978.
Daga 1978 zuwa 1980, ya rike matsayin Kwamishinan Yada Labarai, Harkokin Cikin Gida da Al’adu a tsohuwar Jihar Kano. A lokacin mulkinsa, ya taka rawa wajen kafa jaridar Triumph da gidan talabijin na CTV67, wanda yanzu ake kira ARTV, tare da kula da faɗaɗa ayyukan Radio Kano.

