Kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore ta shiyyar Arewa ta Tsakiya ta roki Shugaba Bola Tinubu da sauran hukumomi su sa baki wajen ganin an saki shugabanta na ƙasa, Abdullahi Bello Bodejo, wanda ke tsare. Kungiyar ta kuma nemi NSA Nuhu Ribadu, Ministan Shari’a Lateef Fagbemi da shugabannin APC da hukumomin tsaro su taimaka wajen sakin Bodejo.
Shugaban kungiyar na Arewa ta Tsakiya, Idris Bebeji, ne ya yi wannan kiran a wani taron manema labarai a Karamar Hukumar Karu ta Jihar Nasarawa. Ya ce Bodejo, wanda ke kare muradun al’ummar Fulani makiyaya, ya taka rawa wajen zaman lafiya, haɗin kan ƙasa da walwalar makiyaya.
Bebeji ya bayyana cewa Bodejo ya fara fuskantar tsarewa ne bayan DSS ta kama shi a Jalingo, Jihar Taraba, a ranar da ya bayyana aniyarsa ta neman kujerar Majalisar Dattawa ta Taraba ta Tsakiya. Ya ce daga bisani aka mika shi ga EFCC, inda ya shafe kusan watanni huɗu, kafin a sake shi sannan DSS ta sake kama shi a ranar 28 ga Agusta 2026.
Kungiyar ta ce ba ta neman a fifita Bodejo sama da doka, sai dai a tabbatar da cewa an bi tsarin doka da hakkokinsa na kundin tsarin mulki. Bebeji ya kuma roki mambobin kungiyar da al’ummar Fulani makiyaya su kwantar da hankula, su ci gaba da bin doka, yayin da ake neman warware lamarin ta hanyar tattaunawa da tsarin kundin tsarin mulki.

