Ɗan takarar shugaban ƙasa na National Democratic Congress, Peter Obi, ya ce ’yan siyasa da rashin kyakkyawan shugabanci ne ke da alhakin matsalolin da Najeriya ke fuskanta. Obi ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi yayin da yake magana a wajen Koinonia Global na Apostle Joshua Selman.
Tsohon gwamnan jihar Anambra ya ce babu wata matsala da Najeriya ke fuskanta, idan ka cire matsalar shugabanci. Ya roƙi mahalarta taron da su riƙa yi wa ’yan siyasa addu’a domin Allah Ya gyara zukatansu, su riƙa amfani da dukiyar gwamnati domin amfanin jama’a.
Obi ya ce arzikin Najeriya zai iya inganta rayuwar ’yan ƙasa tare da magance matsalolin da ake fuskanta idan aka saka shi yadda ya kamata. Ya kuma ce ya ziyarci ƙasashe da dama kuma ya ga yadda tsarin mulki ke aiki a wasu daga cikinsu, yana mai cewa shugabanci ne ya sa kasashe dayawa suka ci gaba.
Obi ya ce yana da yakinin za a iya magance matsalolin Najeriya, matukar shugabanni suka yi abinda ya dace, ya kuma bukaci jama’a da sanya ’yan siyasa da shugabannin ƙasar a cikin addu’o’insu.

