Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da kawo ƙarshen rikicin filaye da ya daɗe tsakanin Jami’ar Bayero Kano (BUK), Rimin Zakara, Rijiyar Zaki da sauran al’ummomin da ke makwabtaka da yankin. Gwamnatin ta ce ta fara aiwatar da cikakken tsarin sasanta rikicin da ya shafe shekaru tun daga shekarun 1980.
Gwamnatin ta ce rikicin ya samo asali ne bayan karɓar filin domin gina harabar dindindin da kuma faɗaɗa Jami’ar Bayero Kano, lamarin da ya haifar da shari’o’i, zanga-zanga, mamaye filaye da matsalolin tsaro. Daga bisani gwamnatin Kano ta kafa wani babban kwamiti domin bincike da tattara bayanai kan rikicin.
A ƙarƙashin sabon tsarin sasantawar, an gano tare da tantance buƙatu da ikirarin mutane sama da 6,000, inda za a ware filayen zama ga waɗanda aka tabbatar da cancantarsu, yayin da ake ci gaba da aiwatar da biyan diyya ga waɗanda suka cancanta.
Gwamnatin ta ce sabon tsarin zai tabbatar da cewa sama da kashi 85 cikin 100 na filayen BUK sun ci gaba da kasancewa domin ayyukan jami’ar na yanzu da na gaba. Ta kuma bayyana cewa biyan diyya ba yana nufin amincewa da cinikin filayen da aka yi tsakanin mutane ba tare da sahihin ikon mallaka ba.
Haka kuma, gwamnatin ta gargaɗi masu sayar da filaye da sauran masu shiga tsakani da su guji anfani da tsarin biyan diyya wajen damfarar jama’a. Ta ce kotu ta tabbatar da matsayin gwamnati kan mallakar filin, yayin da za a fara kwashe gine-gine daga wuraren da doka ta amince gwamnati ta karɓo, tare da gargadin cewa duk wanda ya hana aiwatar da tsarin ko ya sake mamaye filin zai fuskanci hukunci.

