Tawagar tsohon dan takarar gwamnan Jihar Kano, Nasiru Gawuna, ta kai ziyarar goyon baya ga Gwamna Abba Kabir Yusuf da mataimakinsa, Murtala Sule Garo, yayin da ake rade-radin shirin sauya sheƙarsu daga NDC zuwa APC.
Mai magana da yawun Gwamna Abba, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ne ya bayyana ziyarar cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
A cewarsa, tawagar ta ziyarci Gwamna Abba da mataimakinsa ne a yammacin ranar Talata, a matsayin wani bangare na shirye-shiryen komawarsu jam’iyyar APC.
Muhammad Badaru Umar da Ali Datti Yako, wanda aka bayyana a matsayin mataimakin shugaban NDC a jihar, ne suka jagoranci tawagar. Sai dai ba a bayyana lokacin da za a kammala sauya shekar ba, ko adadin magoya bayan da ake sa ran za su koma APC.

