Shugaba Bola Tinubu ya ce Arewacin Najeriya ne zai fi amfana da sauye-sauyen da gwamnatinsa ta kawo, musamman a fannin manyan ayyukan more rayuwa da bunƙasa damar kasuwanci da ƙasashen maƙwabta.
Tinubu ya ce cire tallafin man fetur ya bai wa gwamnati damar karkatar da kuɗaɗen da ake kashewa wajen tallafin zuwa wasu muhimman fannoni na ci gaban ƙasa. Ya bayyana hakan ta bakin Shugaban APC na Ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, a wani taron APC Professionals Forum a Abuja.
Gwamnatin ta ce ayyukan da Arewa za ta amfana da su sun haɗa da bututun iskar gas na Ajaokuta–Kaduna–Kano (AKK), da hanyoyin Akwanga–Maiduguri da Jos–Jalingo, baya ga shirye-shiryen inganta ilimi da horar da matasa.
Sai dai wasu ƙungiyoyin Arewa sun musanta ikirarin. Mai magana da yawun ACF, Farfesa Tukur Muhammad Baba, ya ce kalaman abin mamaki ne, yayin da Dokta Bitrus Pogu ya ce cire tallafin man fetur da amfani da CNG manufofin ƙasa ne baki ɗaya, ba na wani yanki kaɗai ba.

