Shugaban Hukumar Yaƙi da Yiwa Tattalin Arziƙin Ƙasa Zagon Ƙasa (EFCC), Ola Olukoyede, ya bayar da umarnin janye ƙarar da hukumar ta shigar kan Maryam Isah Shehu da Abubakar Shuraim Abdulhamad.
An gurfanar da matasan a gaban Mai Shari’a Joyce Abdulmalik na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ranar Alhamis, 20 ga Agusta 2026, kan zargin aikata laifukan yanar gizo da yaɗa bayanan da EFCC ta ce an yi su ne da nufin ɓata sunan hukumar.
Sai dai Olukoyede ya yi la’akari da roƙon mahaifin Maryam da kuma kiran wasu ‘yan Najeriya na neman a yi wa matasan biyu afuwa, lamarin da ya sa ya bayar da umarnin a janye ƙarar da ake yi musu.
Duk da haka, shugaban EFCC ya gargaɗi cewa hukumar ba za ta ƙara lamuntar duk wani hari na ganganci da ake kai wa mutuncinta ta kowace hanya ko kafar sadarwa ba. Ya kuma tabbatar da cewa hukumar za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta bisa doka da kuma abin da ya dace da muradun ƙasa.

